Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sakataren kwamitin koli na kasar Iran, Ali Larijani, ya tabbatar da kasancewar hannayen Amurka da na Sahayoniya a fili a cikin abubuwan da suke faru a baya-bayan nan a Iran.
Larijani ya fada a wata hira da gidan talabijin na Al-Mayadeen cewa masu tayar da tarzoma na kokari ta hanyar kunna yakin cikin gida, don shire fage ga shiga tsakanin kasashen waje a kasar.
Larijani ya yi ishara da cewa akwai wani yunkuri na waje wanda ke jagorantar rikicin da ake ciki, kuma ya ce: A yakin kwanaki 12, shirinsu shi ne mutane su fito kan tituna, amma ba su yi nasara a hakan ba. Ya kara da cewa, "Trump ya sanar da cewa, idan aka samu rikicin zamantakewa, za mu gudanar da ayyukan soji, wato dabarun Amurka sun canza a yanzu, yayin da suka zo don karya hadin kan jama'a sannan su kai harin soji".
Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar ya bayyana cewa makiyanmu sun yi nufaci babban lamarin, wanda shi ne karfin yakin kwanaki na 12, wanda shi ne hadin kan jama'a.
Ya kara da cewa, "Babu shakka akwai matsalolin tattalin arziki, kuma ya wajaba ga gwamnati da bangarori daban-daban su bi diddigin hakan, amma ya kamata a lura cewa makiya suna bin manufofinsa a bayansa".
Larijani ya bayyana masu tayar da tarzoma a matsayin kungiyoyin ta'addanci kuma ya ce: watanni 3 ko 4 da suka gabata, 'yan sahayoniya sun ce sun samo shirye-shirye a Iran kuma za su yi amfani da su wajen tayar da wata sabuwar kasadar a Iran wadannan sune tsare-tsare da suka samo su.
Larijani ya bayyana cewa, makiya sun nufi yiwa alamar asalin Iran, wadda ita ce tutar Iran, da mutum-mutumin Hajji Qassem, da kuma asalin addini (Masallatai da Alkur'ani), da kuma kwace shi daga hannun jama'a.
Ya yi tambaya: Shin rikicin tsaro yana kara zurfafawa ko rage matsalolin tattalin arziki? Muna da rauni a kasar da kuma cewa wadannan zanga-zangar suna yin tsari a kan wannan batu, amma ya kamata a warware batun ta hanyar da ta da ce saboda sakamakon wadannan zanga-zangar yana cutar da jama'a baki daya kuma ba sa magance wata matsala.
Ya kara da cewa, "Bai kamata mu kyale irin wadannan abubuwa su faru ba, amma idan har tsaron cikin gida na wata kasa ya dame, wajibi ne dakarun soji su shiga fage don kawo karshen rikicin."
Larijani ya ce jami'an tsaro sun gano kwamandojin tarzoma tare da kame wasu daga cikinsu, ciki har da wadanda aka yaudare su, kuma akwai lokuta da dama da sukai amfani da makamai irin su bindigun "C3".
Lokacin da wasu mutane daga cikinsu suke gaggawar zuwa cibiyoyin soja da na 'yan sanda don kwace makamai, hakan na nufin suna neman yakin basasa. Sakataren kwamitin koli na tsaron kasa na Iran ya ce: Babu shakka jami'an tsaro da bangaren shari'a za su yi mu'amala ba tare da hakuri ba ga kungiyoyi masu dauke da makamai da ke son kai hari a cibiyoyin gwamnati da 'yan sanda da kuma kai wa rayuwar 'yan kasa hari.
Ra'ayinka